27
Ceton Isra’ila
1 A wannan rana,
takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna,
zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe,
dodon ruwa macijin nan mai murɗewa;
zai kashe dodon nan na teku.
2 A wannan rana,
“Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce
3 Ni, Ubangiji na lura da ita;
na yi ta yin mata banruwa.
Na yi tsaronta dare da rana
don kada wani yă yi mata ɓarna.
4 Ban yi fushi ba.
Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana!
Zan fita in yi yaƙi da su;
da na sa musu wuta duka.
5 Ko kuma bari su zo wurina don mafaka;
bari su yi sulhu da ni,
I, bari su yi sulhu da ni.”
6 A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa,
Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fure
ya cika dukan duniya da ’ya’ya.
7 Ubangiji ya buge shi
kamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi?
An kashe shi
kamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi?
8 Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi,
da tsananin tsawa kuma ka kore shi,
kamar a ranar da iskar gabas ta hura.
9 A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub,
wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa.
Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade
suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu,
har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare
da za a bari a tsaye.
10 Birni mai katanga ya zama kufai,
yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada;
a can ’yan maruƙa suke kiwo,
a can suke kwance;
sun kakkaɓe rassanta ƙaf.
11 Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su
mata kuma su zo su yi itacen wuta da su.
Gama mutane ne marar azanci;
saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba,
Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.
12 A wannan rana
-
a Da Ibraniyanci Kogi