Zabura 102
Addu’ar mutum mai shan wahala. Sa’ad da ya rasa ƙarfi ya kuma yi makoki a gaban Ubangiji .
1 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji ;
bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka.
2 Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni
sa’ad da nake cikin damuwa.
Ka juye kunnenka gare ni;
sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri.
3 Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi;
ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta.
4 Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa;
na manta in ci abinci.
5 Saboda nishina mai ƙarfi
na rame na bar ƙasusuwa kawai.
6 Ni kamar mujiyar jeji ne,
kamar mujiya a kufai.
7 Na kwanta a faɗake; na zama
kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki.
8 Dukan yini abokan gābana suna tsokanata;
waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana.
9 Gama ina cin toka a matsayin abincina
ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye
10 saboda fushinka mai girma,
gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe.
11 Kwanakina suna kamar inuwar yamma;
na bushe kamar ciyawa.
12 Amma kai, ya Ubangiji , kana zaune a kursiyinka har abada;
sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai.
13 Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona,
gama lokaci ne na nuna alheri gare ta;
ƙayyadadden lokacin ya zo.
14 Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka;
ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi.
15 Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji ,
dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka.
16 Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona
ya kuma bayyana a ɗaukakarsa.
17 Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi;
ba zai ƙyale roƙonsu ba.
18 Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa,
cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji ,
19 “Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa,
daga sama ya hangi duniya,
20 don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku
yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.”
21 Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona
yabonsa kuma a Urushalima
22 sa’ad da mutane da mulkoki
suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada.
23 Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina;
ya gajartar da kwanakina.
24 Sai na ce,
“Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah;
shekarunka suna bi cikin dukan zamanai.
25 A farkon fari ka kafa tushen duniya,
sammai kuma aikin hannuwanka ne.
26 Za su hallaka, amma za ka ci gaba;
duk za su tsufe kamar riga.
Kamar riga za ka canja su
za a kuwa zubar da su.
27 Amma kana nan yadda kake,
kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.
28 ’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka;