Zabura 146
1 Yabi Ubangiji .[~1~]
Yabi Ubangiji , ya raina.
2 Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina;
zan rera yabo ga Allahna muddin raina.
3 Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna,
ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.
4 Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa;
a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.
5 Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa,
wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.
6 Mahaliccin sama da ƙasa,
teku, da kome da yake cikinsu,
7 Yakan biya bukatun mutanen da aka danne
ya kuma ba da abinci ga mayunwata.
8 Ubangiji yakan ba wa makafi ido,
9 Ubangiji yana tsaron baƙi
yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa,
amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.
10 Ubangiji yana mulki har abada,
Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani.
Yabi Ubangiji .
<- Zabura 145Zabura 147 ->
*Zabura 146:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 10.