Zabura 150
1 Yabi Ubangiji .[~1~]
Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;
yabe shi a cikin sammai na ikonsa.
2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;
yabe shi saboda mafificin girmansa.
3 Yabe shi da ƙarar kakaki,
yabe shi da garaya da molo,
4 yabe shi da ganga kuna taka rawa,
yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
5 yabe shi da kuge mai ƙara,
yabe shi da kuge masu ƙara sosai.
6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji .
Yabi Ubangiji .
*Zabura 150:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 6.