Zabura 22
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda.
1 Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?
Me ya sa ka yi nisa da cetona,
ka yi nesa daga kalmomin nishina?
2 Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba,
da dare kuma ban yi shiru ba.
3 Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan;
kai ne yabon Isra’ila.
4 A gare ka ne kakanninmu suka sa bege;
sun dogara ka kuwa cece su.
5 Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto;
a gare ka suka dogara kuma ba su sha kunya ba.
6 Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba,
wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi.
7 Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a;
suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,
8 “Ya dogara ga Ubangiji ;
bari Ubangiji yă cece shi.
Bari yă cece shi,
da yake yana jin daɗinsa.”
9 Duk da haka ka fitar da ni daga ciki;
ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata.
10 Daga haihuwa an jefa ni a kanka;
daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.
11 Kada ka yi nesa da ni,
gama wahala na kusa
kuma babu wani da zai taimaka.
12 Bijimai masu yawa sun kewaye ni;
bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.
13 Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama
sun buɗe bakunansu a kaina.
14 An zubar da ni kamar ruwa,
kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai.
Zuciyata ta zama kaki;
ta narke a cikina.
15 Ƙarfina ya bushe kamar kasko,
harshena kuma ya manne wa dasashina na sama;
ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.
16 Karnuka sun kewaye ni;
ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka,
sun soki hannuwana da ƙafafuna.
17 Zan iya ƙirga ƙasusuwana;
mutane suna farin ciki a kaina.
18 Sun raba rigunana a tsakaninsu
suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.
19 Amma kai, ya Ubangiji , kada ka yi nisa;
Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.
20 Ka ceci raina daga takobi,
raina mai daraja daga ikon karnuka.
21 Ka cece ni daga bakin zakoki;
ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.
22 Zan furta sunanka ga ’yan’uwana;
cikin taron masu sujada zan yabe ka.
23 Ku da kuke tsoron Ubangiji , ku yabe shi!
Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi!
Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!
24 Gama bai rena ko yă ƙyale
wahalar masu shan wuya ba;
bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba
amma ya saurari kukansa na neman taimako.
25 Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro;
a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina.
26 Matalauta za su ci su ƙoshi;
su da suke neman Ubangiji za su yabe shi,
bari zukatanku su rayu har abada!
27 Dukan iyakokin duniya
za su tuna su kuma juya ga Ubangiji ,
kuma dukan iyalan al’ummai
za su rusuna a gabansa,
28 gama mulki na Ubangiji ne
kuma yana mulki a bisa al’ummai.
29 Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada;
dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa,
waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba.
30 Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima;
za a faɗa wa zuriya na nan gaba game da Ubangiji.
31 Za su yi shelar adalcinsa
ga mutanen da ba a riga an haifa ba,