Zabura 29
Zabura ta Dawuda.
1 Ku ba da girma ga Ubangiji , ya ku manya,
ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.
2 Ku ba da girma ga Ubangiji , ɗaukakar da ta dace da sunansa;
ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.
3 Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye;
Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,
4 Muryar Ubangiji mai iko ce;
muryar Ubangiji da girma take.
5 Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon.
6 Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi,
Siriyon[~1~] kuma kamar ɗan jakin jeji.
7 Muryar Ubangiji ta buga
da walƙatar walƙiya.
8 Muryar Ubangiji ta girgiza hamada
9 Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak† Ko kuwa Ubangiji ya sa barewa ta haihu.
ya kakkaɓe itatuwan kurmi.
Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”
10 Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa;
11 Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa;
*Zabura 29:6 Wato, Dutsen Hermon
†Zabura 29:9 Ko kuwa Ubangiji ya sa barewa ta haihu.