Zabura 33
1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;
daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
2 Ku yabi Ubangiji da garaya;
ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
3 Ku rera masa sabuwar waƙa;
ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;
yana da aminci cikin kome da yake yi.
5 Ubangiji yana ƙaunar adalci
duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
6 Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai,
rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
7 Ya tattara ruwan teku cikin tuluna;[~1~]
ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
8 Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji ;
bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
9 Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance;
ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
10 Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai;
yakan wofintar da manufofin mutane.
11 Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada,
manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.
12 Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta ,
mutanen da ya zaɓa don gādonsa.
13 Daga sama Ubangiji ya duba
ya kuwa ga dukan ’yan adam;
14 daga mazauninsa yana lura
da dukan waɗanda suke zama a duniya,
15 shi da ya yi zukatan duka,
wanda yake kula da kome da suke yi.
16 Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa;
ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.
17 Dogara a kan doki don ceto banza ne;
duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.
18 Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
19 don yă cece su daga mutuwa
ya bar su da rai a lokacin yunwa.
20 Muna jiran Ubangiji da bege;
shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
21 A cikinsa zukatanmu na farin ciki,
gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
22 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji ,
ko ma da muke sa begenmu a gare ka.
<- Zabura 32Zabura 34 ->
*Zabura 33:7 Ko kuwa teku sai ka ce a tsibi