Zabura 41
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi;
2 Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa;
zai albarkace shi a cikin ƙasar
ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
3 Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa
ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
4 Na ce, “Ya Ubangiji , ka yi mini jinƙai;
ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
5 Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa,
“Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”
6 Duk sa’ad da wani ya zo ganina,
yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi;
sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.
7 Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina;
suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,
8 “Mugun ciwo ya kama shi;
ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”
9 Har abokina na kurkusa,
wanda na amince da shi,
wanda muke cin abinci tare,
ya juya yana gāba da ni.
10 Amma kai, ya Ubangiji , ka yi mini jinƙai,
ka tā da ni, don in sāka musu.
11 Na sani kana jin daɗina,
gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.
12 Cikin mutuncina ka riƙe ni
ka sa ni a gabanka har abada.
13 Yabo ya tabbata ga Ubangiji , Allah na Isra’ila,
har abada abadin.