Zabura 88
Waƙa ce, Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannot[~1~]maskil[~2~] na Heman dangin Ezra.
1 Ya Ubangiji , Allah wanda ya cece ni,
dare da rana ina kuka a gabanka.
2 Bari addu’ata ta zo a gabanka;
ka kasa kunne ga kukata.
3 Gama raina yana cike da wahala
rayuwata tana gab da kabari.[~3~]
4 An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami;
ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.
5 An ware ni tare da matattu,
kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari,
waɗanda ba ka ƙara tunawa,
waɗanda aka yanke daga taimakonka.
6 Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa
cikin zurfafa mafi duhu.
7 Hasalarka tana da nauyi a kaina;
ka turmushe ni da dukan raƙumanka.
Sela
8 Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni
ka sa na zama abin ƙyama a gare su.
An kange ni, ba yadda zan kuɓuta
9 idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki.
Ina kira gare ka, ya Ubangiji , kowace rana;
na tā da hannuwana zuwa gare ka.
10 Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne?
Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne?
Sela
11 Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne,
ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?
12 An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne,
ko ayyukan adalcinka a lahira?
13 Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji ;
da safe addu’ata kan zo gabanka.
14 Don me, ya Ubangiji , ka ƙi ni
ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?
15 Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu;
na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.
16 Hasalarka ta sha kaina;
razanarka ta hallaka ni.
17 Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa;
sun mamaye ni ɗungum.
18 Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni;
duhu ne abokina na kurkusa.
<- Zabura 87Zabura 89 ->
*^ Kan magana, mai yiwuwa muryar “Tsananin Baƙin Ciki.”
†^ Kan magana, mai yiwuwa kalma waƙa ce.
‡Zabura 88:3 Da Ibraniyanci Sheol