Zabura 9
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda.
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji , da dukan zuciyata;
zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
3 Abokan gābana sun ja da baya;
suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka.
4 Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi;
ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.
5 Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye;
ka shafe sunansu har abada abadin.
6 Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu,
ka tuttumɓuke biranensu;
yadda ma ba aka ƙara tunaninsu.
7 Ubangiji yana mulki har abada;
ya kafa kujerarsa don shari’a.
8 Zai hukunta duniya da adalci;
zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.
9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
mafaka a lokutan wahala.
10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji , ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
11 Rera yabai ga Ubangiji , wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona;
yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.
12 Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna;
ba ya ƙyale kukan masu wahala.
13 Ya Ubangiji , dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini!
Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,
14 don in furta yabanka
cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona
a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.
15 Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu;
aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye.
16 An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa;
an kama mugaye da aikin hannuwansu.
Haggayiyon.
[~2~]Sela
17 Mugaye za su koma kabari,
dukan al’umman da suka manta da Allah.
18 Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba,
ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.
19 Ka tashi, ya Ubangiji , kada ka bar wani yă yi nasara;
bari a hukunta al’ummai a gabanka.
20 Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji ;
bari al’ummai su sani su mutane ne kurum.
Sela
*^ Mai yiwuwa Zabura 9 da 10 tun ainihi waƙa guda ce, ɓangarori mai ƙunshe da layi masu yawa waɗanda suka fara da harufan Ibraniyancin da suke bin juna. A Seftuwajin zabura guda ce.
†Zabura 9:16 Ko kuwa Tunani; mai yiwuwa salon kiɗi ne.