Zabura 93
1 Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka;
An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.
2 An kafa kursiyin tun da daɗewa;
kana nan tun fil azal.
3 Tekuna sun taso, ya Ubangiji ,
tekuna sun ta da muryarsu;
tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.
4 Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye,
mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku,
5 Ƙa’idodinka suna nan daram;
tsarki ya yi wa gidanka ado